‘Yan Majalisar Wakilai Takwas Daga Kano Sun Yi Ficewar Gaggawa Zuwa APC Kwana Daya Bayan Kwankwaso Ya Koma ADC
An sake samun wani babban sauyi a fagen siyasar jihar Kano bayan wasu ‘yan majalisar wakilai takwas daga jihar sun fice daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), sa’o’i 24 kacal bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da komawarsa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC). Rahotanni sun nuna cewa ‘yan majalisar sun bayyana matakin nasu ne a hukumance a Abuja, inda suka ce sun yanke shawarar ficewa daga NNPP sakamakon rikice-rikicen cikin gida da kuma sabbin sauye-sauyen siyasa da ke faruwa a jam’iyyar. ‘Yan majalisar wakilan da suka sauya sheƙa sun jaddada cewa sun koma APC ne domin su ci gaba da wakiltar muradun al’ummominsu yadda ya kamata, tare da samun damar aiki da gwamnatin tarayya wajen kawo ci gaba ga yankunansu. Sun kuma bayyana cewa matakin da suka ɗauka ba shi da alaƙa da wani matsin lamba daga waje, sai dai la’akari da makomar siyasa da kuma muradun jama’ar da suka zaɓe su....