Turkiya Ba Za Ta Amince da Duk Wani Mataki da Zai Haddasa Gaba Tsakanin Al’umman Gabas-ta-Tsakiya Ba -Erdogan
Shugaban ƙasar Turkiya, Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa ƙasar Turkiya ba za ta amince da duk wani mataki da zai haddasa gaba ko ƙiyayya tsakanin al’umman da ke zaune a yankin Gabas ta Tsakiya ba, yana mai jaddada cewa dole ne a kiyaye haɗin kai da zaman lafiya tsakanin ƙasashen yankin.
Erdogan ya ce gwamnatin Turkiya tana da cikakken matsayi na kin goyon bayan duk wani shiri da zai ƙara rarrabuwar kawuna ko haifar da rikici tsakanin ƙasashen da ake ɗauka a matsayin ‘yan’uwa. Ya ƙara da cewa ƙasar sa ba za ta taɓa marawa baya manufofin da ake zargin suna ƙarfafa tsarin “raba kan al’umma domin mulki” ba, wanda ya ce yana barazana ga zaman lafiya da haɗin kan yankin.
Shugaban ya bayyana cewa manufar Turkiya ita ce ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai, da fahimtar juna tsakanin al’ummomi, tare da neman hanyoyin sulhu a maimakon rikici. Ya kuma yi kira ga ƙasashen yankin da su guji duk wani abu da zai iya tayar da rikici ko jefa yankin cikin rashin zaman lafiya.
Maganganun na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar tashin hankali a wasu sassan yankin Gabas ta Tsakiya, inda ƙasashe da dama ke ƙoƙarin nemo mafita mai ɗorewa domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Comments
Post a Comment