Amurka Ta Gargadi Najeriya Kan Kare Kiristoci Bayan Harin Jihar Filato
Ɗan Majalisar Dokokin Amurka, Riley M. Moore, ya yi kakkausar gargaɗi ga gwamnatin Najeriya cewa dangantakar ƙasar da Amurka na iya fuskantar babbar matsala idan ba a ɗauki matakan gaggawa domin kare al’ummar Kiristoci ba, musamman bayan mummunan harin da aka kai a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.
Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari cikin dare a unguwannin da ke cikin ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, inda suka bude wuta kan mazauna garin a lokacin bukukuwan (Palm Sunday).
An ce harin ya jawo asarar rayukan mutane da dama, yayin da wasu da yawa suka jikkata. Haka kuma, mazauna yankin sun tsere daga gidajensu cikin firgici domin neman mafaka a wurare mafi aminci.
Shugabannin al’umma a yankin sun bayyana harin a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya sake tayar da hankulan jama’a kan matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan yankin Arewa ta Tsakiya.
Da yake mayar da martani kan lamarin, ɗan majalisar ya nuna damuwa matuƙa kan yadda ake samun hare-hare kan al’ummar Kiristoci a Najeriya. A saƙon da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X, ya ce:
“Idan ba su ɗauki wannan barazana da muhimmanci ba kuma su tashi tsaye domin kare ‘yan’uwanmu Kiristoci, to jinin waɗannan shahidai zai kasance a wuyansu, kuma hakan zai iya haifar da manyan sakamako ga dangantakar Najeriya da Amurka.”
Bayan harin, hukumomin tsaro a Jihar Filato sun sanar da sanya dokar hana fita a wasu sassan Jos domin daƙile yaɗuwar tashin hankali. Haka kuma, an tura karin jami’an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Jami’an tsaro sun bayyana cewa ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda suka aikata harin tare da kamo su domin su fuskanci hukunci.
Jihar Filato ta daɗe tana fuskantar rikice-rikicen tashin hankali da ake dangantawa da saɓanin kabilanci, addini da rikicin filaye. Masana harkokin tsaro sun jaddada cewa samar da zaman lafiya mai ɗorewa zai buƙaci ɗaukar matakai na dogon lokaci domin magance tushen matsalolin.
Lamarin na baya-bayan nan ya sake jawo hankalin jama’a a cikin gida da ƙasashen waje kan buƙatar ƙara inganta tsaro da kare rayukan fararen hula a Najeriya.
Comments
Post a Comment