APC Ta Fitar da Sabon Tsarin Zaben Shugabanni Gabanin Babban Taro
Jam’iyyar mai mulki ta (APC) ta bayyana tsarin da za ta bi wajen zaben dukkan shugabannin ta na ƙasa gabanin babban taron jam’iyyar da ake shirin gudanarwa.
A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta ce an tsara sahihin matakai da dokoki domin tabbatar da gaskiya da adalci a yayin gudanar da zaɓen shugabannin, tare da bai wa dukkan mambobi damar shiga takara bisa ƙa’ida.
A cewar jam'iyyar, sabon tsarin ya haɗa da sayar da fom ga masu sha’awar takara, tantance ’yan takara domin tabbatar da sun cika sharudda, sannan wakilai daga jihohi da yankuna daban-daban su kaɗa ƙuri’a a yayin babban taron jam’iyyar. Haka kuma, an tanadi kwamitocin da za su kula da tsaro da kuma warware duk wata takaddama da ka iya tasowa bayan zaɓen.
Jam’iyyar ta jaddada cewa sabon tsarin zai taimaka wajen karfafa dimokuraɗiyya a cikin gida, da kuma tabbatar da cewa shugabannin da za a zaɓa sun fito ne ta hanyar sahihin zaɓe wanda ya dace da dokokin jam’iyyar.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa wannan sabon tsari zai taimaka wajen rage rikice-rikice a cikin jam’iyyar tare da samar da shugabanci mai ƙarfi da hadin kai, musamman yayin da ake tunkarar manyan zaɓukan siyasa na gaba.
Ana sa ran babban taron jam’iyyar APC zai tattaro manyan jiga-jigai da wakilai daga sassa daban-daban na ƙasar nan, inda za a zaɓi sabbin shugabannin da za su jagoranci jam’iyyar a mataki na gaba.
Comments
Post a Comment