APC Ta Karyata Labarin Kuɗin Fom Ɗin Zaben 2027, Ta Ce Ƙarya Ce Tsagwaronta
ABUJA, 28 ga Maris, 2026 — Jam'iyyar (APC) ta ƙaryata wani rahoto da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai dangane da farashin fom ɗin nuna sha’awa da takarar zaɓen shekarar 2027, inda ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya kuma mai cike da ruɗani.
A cikin wata sanarwa, wacce Sakataren yaɗa labarai na Ƙasa na jam'iyyar ta APC, Felix Morka, ya sanya wa hannu, aka kuma raba wa manema labarai a ranar Asabar a Abuja, ta ce labarin da ke ɗauke da abin da aka kira “jerin kuɗin fom ɗin zabe na 2027” bai fito daga jam’iyyar ba, kuma ba shi da tushe.
Jam’iyyar ta jaddada cewa har yanzu ba a yanke wani hukunci ko sanar da farashin fom ɗin takara ga zaɓen shekarar 2027 ba, tana mai cewa rahoton da ke yawo ƙirƙirarren labari ne da wani marubuci ya ƙirƙira domin yaɗa ruɗani.
Sanarwar ta ce:
“Jam’iyyar APC tana sanar da cewa rahoton da ake yaɗawa game da farashin fom ɗin nuna sha’awa da takara na zaɓen 2027 ƙarya ce tsagwaronta, kuma bai fito daga jam’iyyar ba. Har yanzu ba a yanke wani hukunci ko sanarwa kan sayar da fom ko farashinsa ba.”
APC ta kuma yi kira ga mambobinta, da kafafen yaɗa labarai da kuma al’umma gaba ɗaya da su yi watsi da rahoton baki ɗaya, tare da gargaɗin a riƙa tabbatar da sahihancin labarai kafin yaɗawa.
Comments
Post a Comment