“Eh, Na Taba Zama Ɗan Fashi Kafin Yesu Ya Kama Ni” — Rev. Dachomo Ya Mayar Wa 'Baba Chinedu" Martani


Shugaban yankin cocin Church of Christ in Nations (COCIN), Rev. Ezekiel Dachomo, ya mayar da martani kan zargin da wani shahararren mai wasan barkwanci ya yi masa cewa ya taba zama ɗan fashi da makami tare da hannu a fashin banki a garin Jos a shekarar 1980.

Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da Baban Chinedu, ya yi kakkausar suka ga Rev. Dachomo a wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, saƙon da tun daga lokacin ya karaɗe shafukan intanet.

A cikin saƙon nasa, Haruna ya zargi Rev. Dachomo da cewa ba wai kawai ya taɓa zama ɗan fashi ba, har ma ya ƙirƙiri labarin haɗuwarsa da Yesu Kristi domin ya yaudari jama'a. Ya kuma yi iƙirarin cewa akwai bayanai tun daga shekarar 1976 da ke nuna cewa malamin ya kasance cikin harkar fashi na tsawon lokaci.

Sai dai a nasa ɓangaren, Rev. Dachomo ya amsa zargin da cewa gaskiya ne ya taɓa shiga harkar fashi a baya, amma ya ce ya daina ne bayan ya tuba, yana mai cewa “Yesu ne ya kama shi” wato ya sauya masa rayuwa gaba ɗaya.

Malamin ya bayyana cewa sauyin da ya samu ya faru ne bayan wani lamari mai girma da ya faru da shi bayan fashin banki a Jos a shekarar 1980, wanda daga nan ne ya rungumi addini tare da sadaukar da rayuwarsa wajen wa’azi da hidimar coci.

Lamarin ya jawo cece-kuce a tsakanin jama'a, musamman a jihohin Arewa, musamman jihar Filato inda wasu ke ganin furucin nasa hujja ce ta yadda mutum zai iya tuba ya gyara rayuwarsa, yayin da wasu ke ci gaba da tambayar gaskiyar tarihin da ake ta muhawara a kai.

Ana sa ran ƙarin bayani zai ci gaba da fitowa yayin da muhawarar ke ƙara daukar zafi a kafafen sada zumunta.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO