‘Yan Majalisar Wakilai Takwas Daga Kano Sun Yi Ficewar Gaggawa Zuwa APC Kwana Daya Bayan Kwankwaso Ya Koma ADC
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan majalisar sun bayyana matakin nasu ne a hukumance a Abuja, inda suka ce sun yanke shawarar ficewa daga NNPP sakamakon rikice-rikicen cikin gida da kuma sabbin sauye-sauyen siyasa da ke faruwa a jam’iyyar.
‘Yan majalisar wakilan da suka sauya sheƙa sun jaddada cewa sun koma APC ne domin su ci gaba da wakiltar muradun al’ummominsu yadda ya kamata, tare da samun damar aiki da gwamnatin tarayya wajen kawo ci gaba ga yankunansu.
Sun kuma bayyana cewa matakin da suka ɗauka ba shi da alaƙa da wani matsin lamba daga waje, sai dai la’akari da makomar siyasa da kuma muradun jama’ar da suka zaɓe su.
Wannan sauyi ya zo ne a daidai lokacin da siyasar jihar Kano ke fuskantar girgiza mai ƙarfi, musamman bayan komawar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daga NNPP zuwa jam’iyyar ADC, lamarin da ya haifar da muhawara da ce-ce-ku-ce a tsakanin magoya baya da ‘yan siyasa.
Masana siyasa na ganin cewa sauyin sheƙar da ‘yan majalisar wakilan suka yi na iya ƙara sauya fasalin siyasar Kano da ma yankin Arewa gaba ɗaya, musamman yayin da ake tunkarar zabukan shekarar 2027.
Har yanzu dai shugabannin jam’iyyar NNPP a jihar Kano ba su fitar da cikakken martani ba kan wannan lamari, amma wasu jiga-jigan jam’iyyar na kokarin kwantar da hankalin magoya bayansu tare da tabbatar da cewa jam’iyyar za ta ci gaba da kasancewa mai ƙarfi duk da irin waɗannan sauye-sauye.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana cewa wannan jerin sauye-sauyen na nuna yadda siyasar Najeriya ke shiga wani sabon salo na sauya sheƙa, wanda ka iya yin tasiri sosai a taswirar siyasa kafin babban zaɓen ƙasa mai zuwa.
Comments
Post a Comment