Jam'iyyar PDP Za Ta Ba Da Mamaki A zaɓe Mai Zuwa - Inji Wike
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa jam’iyyar (PDP) za ta ba da mamaki a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Wike ya ƙara da cewa jam'iyyar ta PDP za ta gudanar da babban taronta na ƙasa kamar yadda aka tsara a ranakun 29 da 30 ga watan Maris.
Ya bayyana haka ne yayin da ake ci gaba da samun saɓani tsakanin wasu mambobin jam’iyyar, inda ya ce duk da matsalolin cikin gida, shugabannin PDP sun ƙuduri aniyar ci gaba da shirye-shiryen taron domin tabbatar da ɗorewar dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyar.
Ya kuma jaddada cewa ƙoƙarin sulhu da mambobin da suke da ƙorafi zai ci gaba bayan kammala babban taron, domin dawo da haɗin kai da zaman lafiya a cikin jam’iyyar.
Ministan ya ƙara da cewa shugabannin PDP suna da yaƙinin cewa taron zai gudana cikin nasara, tare da samar da sabbin tsare-tsare da za su ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓukan gaba.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa wannan sanarwa na Wike na nuni da aniyar shugabannin PDP na ci gaba da tafiyar da al’amuran jam’iyyar duk da ƙalubalen da take fuskanta a halin yanzu.
Comments
Post a Comment