ADC Ta Aika Saƙo Mai Zafi Ga Tinubu Yayin Cikarsa Shekara 74
Jam’iyyar adawa ta (ADC) ta aika saƙo mai cike da suka ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yayin da yake cika shekaru 74 a duniya, tana mai cewa alƙawarin “Ƙariya” da ya yi wa ‘yan Najeriya ya koma wahala ga al’umma.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Jam’iyyar na Ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi, jam’iyyar ta ce duk da cewa tana taya shugaban ƙasa murnar zagayowar ranar haihuwarsa, ya kamata ya yi nazari kan halin da ƙasar ke ciki da kuma matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
Jam’iyyar ta bayyana cewa hauhawar farashin man fetur da tsadar rayuwa sun sanya rayuwa ta ƙara tsananta ga talakawan Najeriya, inda ta ce iyalai da dama suna fuskantar matsin rayuwa mai tsanani.
ADC ta ce:
“Yawancin ‘yan Najeriya sun shiga cikin ƙunci sakamakon manufofin gwamnati, musamman bayan cire tallafin man fetur, wanda ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki da sufuri.”
Har ila yau, jam’iyyar ta yi zargin cewa matsalar tsaro ta ƙara kamari a sassa daban-daban na ƙasar, inda ta ce hare-haren ‘yan bindiga da sauran rikice-rikice sun ci gaba da janyo asarar rayuka da raba jama’a da muhallansu.
Ta ƙara da cewa rahotanni na duniya sun nuna cewa Najeriya na cikin ƙasashen da matsalar ta’addanci ke ƙaruwa, lamarin da ya kamata gwamnati ta ɗauka da muhimmanci.
A ƙarshe, jam’iyyar ADC ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya yi amfani da wannan lokaci na cika shekaru 74 wajen yin tunani mai zurfi kan shugabancinsa, tare da ɗaukar matakai masu inganci domin rage wahalar tattalin arziki da inganta tsaro a ƙasar.
Jam’iyyar ta kuma yi masa fatan alheri tare da addu’ar Allah ya ba shi hikima da ƙarfi wajen jagorantar ƙasar cikin adalci da nasara.
Comments
Post a Comment