Yadda Sojoji Suka Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Bayan 'Yan Bindiga Sun Harbe Ta a Katsina

Majiyoyin soji sun bayyana cewa 'yan bindiga sun harbi matar marigayi tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar tare da tserewa bayan dakarun soji sun yi arangama da su a ƙauyen Tunga da ke Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina.

Rahotanni sun ce dakarun Operation FANSAN YANMA sun samu nasarar ceto matar, duk da cewa tana zubar da jini sakamakon harbin da aka yi mata. An ba ta agajin gaggawa a wurin kafin a garzaya da ita zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

A cewar majiyoyin tsaro, farmakin ceto ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu kan masu garkuwa da mutane, lamarin da ya sa sojoji suka matsa musu har suka watse suka gudu.

An kuma bayyana cewa dakaru na ci gaba da farautar 'yan bindigar da ake zargin suna da hannu a harin da kuma sace-sacen da suka gabata, yayin da ake ci gaba da gudanar da samamen kawar da maboyarsu a yankin.

Hukumomin tsaro sun jaddada kudurinsu na kamo duk masu hannu a wannan ta'asa tare da tabbatar da an gurfanar da su gaban shari'a.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO