VDM Ya Jagoranci Zanga-Zanga Zuwa Gidan Gwamna Makinde, Don Neman Sakin Ɗalibai da Malaman da Aka Sace a Oyo
Shahararren mai fafutukar kafafen sada zumunta, Martins Vincent Otse wanda aka fi sani da (VDM), ya jagoranci masu zanga-zanga zuwa gidan Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, da ke Ibadan domin matsa lamba kan gwamnati ta gaggauta ceto ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Oriire.
Masu zanga-zangar sun bayyana damuwa kan yadda waɗanda aka sace ke ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da mutane, inda suka buƙaci gwamnati da jami’an tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin tabbatar da sakin su cikin ƙoshin lafiya.
VDM ya ce rayukan yaran makaranta da malamansu na cikin haɗari, yana mai kira ga Gwamna Makinde da gwamnatin tarayya su ƙara ƙaimi wajen gudanar da aikin ceto.
Lamarin ya janyo hankalin jama'a a faɗin ƙasar nan, yayin da iyalai da al'ummomin yankin ke ci gaba da jiran samun labarin kubutar waɗanda aka sace. #BreakingNews #Oyo #VDM #Makinde #Kidnapping #Oriire #ZanceNyau247
Comments
Post a Comment