Mutum Daya Ya Mutu, Bakwai Sun Jikkata Bayan Fashewar Bam a Hanyar Zamfara
Wani mutum ya rasa ransa yayin da wasu mutum bakwai suka jikkata sakamakon fashewar wani bam da aka dasa a gefen hanya a Jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da matafiya ke wucewa ta hanyar, inda bam ɗin ya fashe ba zato ba tsammani, lamarin da ya haddasa ruɗani da firgici a tsakanin masu amfani da hanyar da mazauna yankin.
Shaidun gani da ido sun ce fashewar ta yi ƙarfi matuƙa, inda ta jawo asarar rai tare da raunata mutane da dama. An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci domin samun kulawar likitoci, yayin da jami’an tsaro suka isa wurin domin daƙile yiwuwar sake afkuwar makamancin lamarin.
Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yadda ƙungiyoyin ‘yan bindiga ke amfani da bama-bamai da aka ƙera cikin gida wajen kai hare-hare a wasu sassan Arewa maso Yammacin Najeriya.
Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa amfani da irin waɗannan bama-bamai na nuna sabon salo da miyagun ƙungiyoyi ke ɗauka wajen aiwatar da hare-harensu, abin da ke ƙara jefa matafiya da mazauna yankunan karkara cikin haɗari.
A halin yanzu, jami’an tsaro sun fara bincike domin gano waɗanda ke da hannu a harin tare da share hanyar daga duk wani abin fashewa da ka iya jefa rayukan jama’a cikin haɗari.
Hukumomi sun kuma yi kira ga al’umma da su kasance cikin shiri tare da kai rahoton duk wani abu ko motsi da suka gani mai tayar da hankali ga jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.
Comments
Post a Comment