Kachalla Muhammad Ya Tuntuɓi Iyalan Janar da Aka Sace, Ya Gabatar da Sharadi

Shahararren jagoran 'yan bindiga, Kachallah Muhammad, ya buɗe hanyar sadarwa da iyalan tsohon babban hafsan soja mai ritaya, Manjo Janar Rabe Abubakar Batsari, wanda aka yi garkuwa da shi a Jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa Kachallah Muhammad ya ba iyalan Janar damar yin magana da shi, inda Janar ɗin ya tabbatar da cewa yana cikin ƙoshin lafiya tare da matarsa.

Wata majiya daga ƙaramar hukumar Batsari ta ce jagoran 'yan bindigar ya gabatar da sharaɗi, yana neman a saki wasu daga cikin 'yan uwansa da yake zargin suna tsare a hannun jami'an tsaro.

Har yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan wannan buƙata ba, yayin da ake ci gaba da sa ido kan lamarin.

#Katsina #GarkuwaDaMutane #KachallahMuhammad #BreakingNews #ZancenYau247

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO