Kotu Ta Yanke Wa Mahaifiya Da Ƙanwar Fitaccen Ɗan Ta'adda Hukuncin Shekara 20 a Gidan Yari
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Safiya Salihu, mahaifiyar fitaccen shugaban 'yan bindiga Kachallah Ibrahim Battujo, da kuma Halima Abdullahi, ƙanwarsa, hukuncin shekara 20 a gidan yari bayan sun amsa laifukan da suka shafi taimakawa ayyukan ta'addanci.
Alkalin kotun, Mai Shari'a Hauwa Yilwa, ta yanke hukuncin ne bayan mutanen biyu sun amsa laifuffuka uku cikin tuhume-tuhume biyar da Ofishin Babban Lauyan Tarayya (AGF) ya shigar a kansu.
Binciken da Hukumar DSS ta gudanar ya nuna cewa sun kasance suna bai wa Battujo bayanai ta wayar salula tare da ɓoye wasu muhimman bayanai da suka shafi ayyukansa na ta'addanci. Haka kuma, Halima ta amsa cewa ta ɓoye bayanin mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba da ɗan'uwanta ke yi.
Kotun ta janye tuhume-tuhume biyu da suka shafi karɓar kuɗin da ake zargin an samo daga ta'addanci da kuma tafiyar aikin Hajji da irin waɗannan kuɗaɗe, bayan buƙatar masu gabatar da ƙara.
Ko da yake kotun ta bayyana hukuncin shekaru 40 ne gaba ɗaya, ta umurci a haɗa hukuncin, wanda ke nufin kowacce daga cikinsu za ta yi shekara 20 kacal a gidan yari, sannan bayan kammala wa'adin za a tura su shirin gyaran hali.
Comments
Post a Comment