KANO TA ZAMA JIHAR DA TA FI DACEWA IYALI ZAMA A NIGERIYA – RAHOTO

Wani sabon rahoto da kamfanin bincike na SBM Intelligence ya fitar ya bayyana cewa Jihar Kano ce ta zama jihar da ta fi dacewa iyalai zama a Najeriya a shekarar 2026.

Rahoton ya nuna cewa Kano ta zarce jihohi masu arziki kamar Legas, Ribas da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja wajen tsaro, arahar rayuwa, kula da yara, samar da wutar lantarki da kuma haɗin kan al’umma.

Masu binciken sun bayyana cewa duk da cewa yawancin mazauna Kano na samun ƙananan kuɗaɗen shiga idan aka kwatanta da wasu jihohi, arahar rayuwa da yanayin tsaro sun taimaka wajen inganta rayuwar iyalai.

Rahoton ya kuma nuna cewa Kano ce ta samu mafi girman maki a fannin tsaro, inda mafi yawan mazauna jihar suka ce suna jin kwanciyar hankali ko da bayan dare.

A cewar SBM Intelligence, samun ingantaccen tsaro, sauƙin kula da yara, arahar gidaje da kuma ƙarfin dangantakar al’umma ne suka sa Kano ta zama wuri mafi dacewa ga iyalai a Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO