Kaduna – Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne da suka yi iƙirarin tuba sun kai hare-hare biyu a yankin Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, inda suka kashe jikan wani Hakimi tare da yin garkuwa da mutum tara.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin na farko ya faru ne a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, inda maharan suka tare wata mota a kusa da Kwanan Giginya. Sun bude wa motar wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Malam Ibrahim Adamu, wanda aka ce jikan wani Hakimi ne a masarautar Birnin Gwari.

Bayan kashe shi, maharan sun yi awon gaba da fasinjoji biyar da ke cikin motar kafin su tsere zuwa cikin daji.

A wani hari daban da aka kai a yankin Kurgi, 'yan bindigar sun kutsa cikin gonaki inda suka yi garkuwa da wasu manoma huɗu yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Wannan sabon hari ya ƙara tayar da hankalin mazauna yankin, musamman ganin cewa wasu daga cikin maharan ana zargin suna cikin waɗanda suka yi alƙawarin ajiye makamai tare da rungumar zaman lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO