Iyayen Daliban Da Aka Sace a Oyo Sun Ki Karɓar Shinkafa Da Kuɗi, Sun Nemi A Dawo Da 'Ya'yansu
Iyayen ɗalibai da malamai da aka sace a Jihar Oyo sun ƙi karɓar tallafin shinkafa da kuɗi da gwamnati ta kai musu, inda suka bayyana cewa abin da suka fi buƙata shi ne a ceto 'ya'yansu cikin ƙoshin lafiya.
Sarkin gargajiyar yankin Yawota, Emmanuel Alade, ya ce iyalan waɗanda aka sace sun nuna rashin jin daɗinsu da halin da ake ciki, suna masu cewa babu wani tallafi da zai maye gurbin dawowar 'ya'yansu gida.
Rahotanni sun nuna cewa ɗalibai da malamai da dama ne 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a wasu al’ummomin Ƙaramar Hukumar Oriire da ke jihar.
Duk da ziyarar jami’an gwamnati da alkawarin ƙara ƙaimi wajen ceto waɗanda aka sace, iyayen sun jaddada cewa babban burinsu shi ne ganin an dawo da 'ya'yansu lafiya cikin gaggawa.Wannan labari na ci gaba da janyo hankalin al’umma yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kubutar da waɗanda aka sace.
Comments
Post a Comment