Gaggawar Labarai: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masaukin Dalibai a Zamfara, Sun Sace 7
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari masaukin daliban Zamfara State College of Arts and Science (ZACAS) da ke Gusau, inda suka yi garkuwa da ɗalibai bakwai a wani hari da suka kai da daddare.
Rahotanni sun ce maharan sun kutsa cikin ɗakunan kwanan daliban ne ɗauke da makamai, suka tafi da ɗaliban zuwa wani wuri da ba a sani ba. Sai dai ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ya samu damar tserewa daga hannun ‘yan bindigar yayin da ake tafiya da su.
A halin yanzu, ɗalibai shida na ci gaba da kasancewa a hannun maharan, yayin da jami’an tsaro suka fara bincike da ƙoƙarin ceto su.
Lamarin ya sake tayar da hankalin jama'a kan matsalar rashin tsaro da ke addabar makarantu da al’ummomi a wasu sassan jihar Zamfara.
— ZancenYau247
Comments
Post a Comment