Fashewar Bam a Hanyar Bagega–Anka Ta Hallaka Mutane 10, Ta Jikkata 7 a Zamfara
ANKA, ZAMFARA – Aƙalla mutane goma sun rasa rayukansu yayin da wasu bakwai suka jikkata sakamakon fashewar wani bam da ake zargin na'urar fashewa ce ta IED (Improvised Explosive Device) a kan hanyar Bagega zuwa Anka da ke Jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da wata motar ɗaukar fasinjoji ke wucewa ta hanyar, inda bam ɗin ya fashe tare da haddasa mummunar asara ga rayuka da dukiyoyi.
Shaidu sun ce ƙarfin fashewar ya jefa fasinjoji cikin mawuyacin hali, inda wasu suka mutu nan take yayin da aka garzaya da waɗanda suka samu raunuka zuwa cibiyoyin lafiya domin samun kulawar gaggawa.
Bayan aukuwar lamarin, jami'an tsaro sun bazama yankin tare da kara tsaurara matakan tsaro domin hana sake afkuwar irin wannan hari. Haka kuma, kwararrun jami'an binciken abubuwan fashewa sun fara aikin bincike domin gano yadda aka dasa bam din da kuma wadanda ke da hannu a kai.
Mahukunta sun buƙaci mazauna yankin da matafiya su kasance cikin shiri tare da bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro domin taimakawa wajen daƙile ayyukan masu tada ƙayar baya.
Lura: Rahotannin da aka tabbatar daga hukumomi sun nuna mutum daya ya mutu sannan bakwai suka jikkata a sabon harin da ya faru a hanyar Anka–Bagega, yayin da bincike ke ci gaba.
Comments
Post a Comment