DSS Ta Gano Shirin ‘Yan Ta’adda Na Sace Dalibai Da Yawa A Edo, Gwamnati Ta Rufe Makarantu

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta yi gargaɗin cewa wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne na shirin kai hare-hare tare da yin garkuwa da ɗaliban makarantu da yawa a Jihar Edo, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ɗauki matakan gaggawa domin kare rayuka.

Wani bayanin sirri da ya fito daga DSS ya nuna cewa jami’an tsaro sun samu bayanan sirri kan wani shiri da wasu da ake zargi da kasancewa masu garkuwa da mutane suka ƙulla domin sace ɗalibai musamman a yankin Edo Ta Arewa. Rahotanni sun ce an gano shirin ne bayan jami’an tsaro sun sa ido kan tattaunawar wasu da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci.

A cewar bayanan, waɗanda ake zargin sun yanke shawarar mayar da hankali kan sace ɗalibai ne bayan yunƙurin su na yin garkuwa da attajirai bai samar musu da kuɗin fansa da suke nema ba. Sun yi imanin cewa sace ɗalibai zai jawo hankalin gwamnati tare da ƙara yiwuwar samun manyan kuɗaɗen fansa.

Rahoton ya kuma bayyana cewa an kama wani matashi mai suna Emmanuel Momidu mai shekaru 25 a kusa da Makarantar Sakandaren Makeke da ke karamar hukumar Akoko-Edo, inda ake zargin yana gudanar da binciken sirri kan makarantar kafin kai harin. Wannan kama ya ƙara tabbatar da fargabar cewa shirin na iya kasancewa a matakin aiwatarwa.

Sakamakon wannan barazana, gwamnatin Jihar Edo ta ba da umarnin rufe wasu makarantu uku da ke yankin Akoko-Edo domin kare ɗalibai da malamai daga duk wata barazana. Duk da rufe makarantun, ɗaliban da ke rubuta jarabawar WASSCE za su ci gaba da rubuta jarabawarsu ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.

DSS ta buƙaci a ƙara tsaro a makarantu, a tura jami’an tsaro zuwa wuraren da ake ganin suna cikin haɗari, tare da haɗin gwiwar masu sintiri, mafarauta da sauran jami’an tsaro domin hana duk wani yunkurin kai hari.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO