DA DUMI-DUMI: Gwamna Makinde Ya Bauyana Wurin Da Aka Ɓoye Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya jawo hankalin ‘yan Najeriya bayan ya bayyana bayanan da suka shafi wurin da ake zargin masu garkuwa da mutane suka boye dalibai da malamai da aka sace a hare-haren da aka kai makarantu a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun kai hare-hare a makarantu uku da ke yankin Oriire na Jihar Oyo a ranar 15 ga Mayu, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da malamai da dama. Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa aƙalla ɗalibai 25 da malamai bakwai ne aka sace yayin harin.

Makinde ya bayyana cewa bayanan sirri da jami’an tsaro suka tattara sun nuna cewa ana zargin an kai waɗanda aka sace zuwa cikin dazukan Old Oyo National Park, wani babban yankin daji da ya mamaye sassan Jihar Oyo da maƙwabtan jihohi. 

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar na aiki kafaɗa da kafaɗa da rundunar sojoji, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da ceto ɗaliban da malamansu cikin ƙoshin lafiya. Ya kuma bayyana cewa an kama wasu da ake zargi da taimakawa masu garkuwa da mutanen, yayin da bincike ke ci gaba.

A halin yanzu, gwamnatin Oyo ta buƙaci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da kauce wa yaɗa jita-jita, tana mai tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an kuɓutar da ɗaliban da malamansu cikin gaggawa.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO