An Dakile Harin 'Yan Bindiga a Zamfara, An Hallaka Shida
Maru, Zamfara – Rundunar haɗin gwiwa ta jami'an tsaro ta samu nasarar daƙile wani yunƙurin hari da 'yan bindiga suka kai kan al'ummomin Kanoma da Gidan Daji da ke ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara, inda aka kashe mutum shida daga cikin maharan.
A cewar rundunar 'yan sanda ta Jihar Zamfara, maharan sun kutsa cikin yankunan ne dauke da manyan makamai, ciki har da RPG, bindigogin GPMG, manyan bindigogin harbo jiragen sama da kuma bindigogin AK-47, da nufin kai hari kan al'ummomin biyu.
Sai dai jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji, 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun yi gaggawar mayar da martani, lamarin da ya haddasa mummunar musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron sun yi nasarar kashe 'yan bindiga shida, yayin da wasu da dama suka tsere cikin daji dauke da raunukan harbin bindiga.
Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa babu wani jami'in tsaro ko farar hula da ya rasa ransa a wannan samame, yayin da ake ci gaba da sintiri da farautar sauran maharan da suka tsere domin hana sake kai hare-hare a yankin.
Jami'an tsaro sun kuma yi kira ga mazauna yankunan da su ci gaba da bai wa hukumomi sahihan bayanan sirri domin ƙarfafa yaki da matsalar tsaro a jihar.
Comments
Post a Comment