Zargin Kashe Dadiyata: Sabuwar Maganar Muhammad Musa Ta Janyo Cece-kuce
Wani lauya mai zaman kansa a Kano, wato Bello Iliyasu ya bayyana shakku kan sabon ikirarin da tsohon hadimin ƙaramin ministan tsaro, wato Muhammad Musa ya yi, inda ya ce jami’an tsaro ne suka kashe ɗan gwagwarmayar neman sauyi, Abubakar Idris Dadiyata.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Bello Iliyasu ya bayyana cewa Muhammad Musa ya taɓa kasancewa memba a kwamitin sulhu da gwamnatin jihar Zamfara ta kafa domin sasanta rikici tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga.
Lauyan ya kuma tuna cewa jami’an ‘yan sanda sun taɓa kama Muhammad Musa bisa zargin ta’addanci, da satar shanu, da garkuwa da mutane da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
A cewarsa, rundunar ‘yan sanda ƙarƙashin jami’i Hassan Gimba ta taba wallafa wani bidiyo da ke nuna Muhammad Musa yana amsa tambayoyi tare da bayyana alaƙar sa da fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji.
Sai dai daga baya Muhammad Musa ya ce an tilasta masa yin furucin da ke cikin bidiyon, lamarin da ya haddasa saɓani tsakaninsa da jami’an tsaron.
Rahotanni sun nuna cewa an gurfanar da Muhammad Musa tare da Bello Turji da wasu mutum huɗu a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa tuhume-tuhume da suka haɗa da garkuwa da mutane da wasu manyan laifuka guda 11.
Yanzu haka dai sabon ikirarin da Muhammad Musa ya yi na cewa jami’an tsaron da suka kama shi su ne suka kashe Dadiyata ya sake tayar da ƙura a kafafen sada zumunta da kuma tsakanin masu bibiyar batun ɓacewar Dadiyata.
Sai dai Bello Iliyasu ya bayyana cewa bai yarda da wannan ikirari ba, yana mai kira da a zurfafa bincike domin gano haƙiƙanin waɗanda ke da hannu a ɓacewar Dadiyata.
Har zuwa yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ‘yan sanda kan sabon zargin da Muhammad Musa ya yi.
Comments
Post a Comment