Tagwaye a Birtaniya Sun Gano Suna da Ubanni Daban-Daban
London, Birtaniya – Wasu mata tagwaye, Lavinia da Michelle Osbourne, sun gano cewa suna da ubanni mabambanta, a wani lamari da masana kimiyya ke kira heteropaternal superfecundation, wanda ake ɗauka a matsayin mai matuƙar wuya.
Rahotanni sun nuna cewa wannan yanayi na faruwa ne idan mace ta fitar da ƙwayayen haihuwa biyu a lokaci guda, sannan kowane ɗaya ya haɗu da maniyyi daga maza daban cikin ɗan gajeren lokaci. A irin wannan hali, ana iya haifar tagwaye da ba su da uba guda, duk da cewa suna da uwa ɗaya.
An ce ‘yan uwan, masu shekaru kusan 49, sun fara samun shakku kan asalinsu ne bayan sun yi gwajin ƙwayoyin halitta (DNA). Sakamakon gwajin ya nuna cewa kowacce daga cikinsu na da mahaifi daban, lamarin da ya tabbatar da cewa ba cikakkun tagwaye ba ne, sai dai ‘yan’uwa masu rabin jini.
Masana sun bayyana cewa irin wannan lamari na da matuƙar ƙaranci a duniya, inda aka ce ba a fi samun irin sa sau da dama ba. Wannan shi ne karo na farko da aka tabbatar da irin wannan a Birtaniya.
An wallafa wannan labari ne a wani shiri na gidan rediyon BBC, inda ya ja hankalin jama’a a faɗin duniya.
Comments
Post a Comment