Rikicin Siyasar Rivers Ya Ƙara Zafi: Jagoran ‘Yan Adawar PDP a Majalisa Ya Bayyana Gaban Kwamitin Tantance ‘Yan Takarar APC

Rahotanni da ke yawo sun bayyana cewa jagoran ‘yan adawa na jam’iyyar PDP a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Kingsley Chinda, ya bayyana a gaban kwamitin tantance ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC domin zaɓen gwamnan jihar Rivers na shekarar 2027.

Chinda, wanda a halin yanzu yake wakiltar jam’iyyar People's Democratic Party (PDP) a Majalisar Tarayya, an ce ya shiga tantancewar ne a matsayin ɗan takarar gwamna karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Rahotannin sun kuma nuna cewa akwai jita-jitar cewa ɗan majalisar ya sauya sheƙa zuwa APC cikin sirri a kwanakin baya, duk da cewa har yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da hakan.

Majiyoyi sun bayyana cewa Chinda na daga cikin ƙusoshin siyasar ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da suka sayi fom ɗin takarar gwamna na APC. Ana zargin cewa wani na kusa da Wike mai suna Dax Kelly shi ma ya sayi fom ɗin.

Sauran fitattun ‘yan siyasar da ake cewa sun sayi fom ɗin sun haɗa da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da tsohon ɗan takarar gwamna na APC, Tonye Cole.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO