Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi Sun Yi Zanga-Zanga a Borno Kan Rashin Aiwatar da Mafi Ƙarancin Albashi na N70,000
Ma’aikatan ƙananan hukumomi a Jihar Borno sun fito kan titunan Maiduguri a ranar Juma’a domin nuna rashin amincewarsu da gazawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa na N70,000.
Zanga-zangar, wadda ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka shirya a matsayin wani ɓangare na bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya, ta bayyana tsananin halin ƙunci da ma’aikatan ke ciki.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago na jihar, Yusuf Inuwa, ya ce ma’aikatan ƙananan hukumomi su ne suka fi shan wahala a halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki, yana mai cewa sun zaɓi yin bikin ranar ma’aikata ne a kan tituna domin nuna damuwarsu.
Ya bayyana cewa duk da gwamnatin jihar ta fara aiwatar da sabon albashi ga malamai da ma’aikatan lafiya, har yanzu ma’aikatan ƙananan hukumomi da dama ba a shigar da su cikin tsarin ba.
A cewarsa, albashin da suke karɓa ba ya iya ɗaukar buƙatunsu na mako guda, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen wannan halin.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar ta danganta jinkirin aiwatar da sabon albashin da yawan ma’aikatan ƙananan hukumomi da ya kai kusan 90,000 a faɗin ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Comments
Post a Comment