🚨 LABARIN GAGGAWA: Ɗan El-Rufai a Majalisar Wakilai Ya Fice Daga APC Zuwa ADC
ÆŠan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kuma É—an majalisar wakilai mai wakiltar Kaduna North, Bello El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC.
Rahotanni sun bayyana cewa Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ne ya karanta wasiƙar sauya shekar Bello El-Rufai a zaman majalisar na ranar Alhamis.
Baya ga Bello El-Rufai, wasu ‘yan majalisa biyu daga jihar Kaduna — Umar Ajilo da Suleiman Richifa — suma sun bar PDP zuwa ADC, yayin da wasu ‘yan majalisa suka koma sabbin jam’iyyu daban-daban.
Majiyoyi sun ce ‘yan majalisar sun danganta matakin nasu da rikice-rikicen cikin gida da rashin tabbas da ke addabar tsofaffin jam’iyyunsu.
Sauya shekar Bello El-Rufai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓen 2027, lamarin da ke ƙara girgiza APC musamman a jihar Kaduna.
Comments
Post a Comment