Hukumar Kula da Ƙa'idoji Ta Ba NAPRI Yoghurt Takardar Shaidar Inganci
Hukumar Kula da Ka'idoji da nagarta ta Ƙasa (SON) ta bai wa NAPRI Yoghurt, wani samfurin madara da Ma'aikatar Binciken Dabarun Samar da Dabbobi ta ƙasa, wato NAPRI, da ke Jami'ar Ahmadu Bello, ta ke samarwa takardar shaidar cika ƙa'idojin inganci, tsafta da tsaro.
Wannan shi ne karo na farko da wani samfurin madara da NAPRI ta samar ya samu wannan matsayi. Jami'an cibiyar sun bayyana nasarar a matsayin babbar cigaba ga masana'antar madara, wadatar abinci da kuma bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.
NAPRI ta ce samun takardar shaidar zai ƙara wa madarar karɓuwa a kasuwa tare da tallafa wa manufar gwamnatin tarayya na bunƙasa amfani da kayayyakin cikin gida.
Comments
Post a Comment