Gwamnatin Zamfara ta Fara Biyan Tsofaffin Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi Naira Miliyan 499
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da fara biyan kuɗaɗen fansho da garatuti ga rukuni na uku na tsofaffin ma’aikatan ƙananan hukumomi na shekarar 2025, inda ta ware jimillar Naira miliyan 499 domin biyan haƙƙoƙinsu.
Haka kuma, gwamnatin ta sanar da fara saka sauran tsofaffin ma’aikatan da ba a taɓa shigar da su cikin tsarin biyan fansho ba domin su fara karbar albashinsu na wata-wata.
Kwamishinan Ma’aikatar ƙananan hukumomin jihar Zamfara, Injiniya Ahmad Garba Yandi, ya bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na inganta rayuwar masu ritaya tare da tabbatar da cewa sun samu haƙƙoƙinsu cikin lokaci.
Ya ce an gudanar da tantancewa da bincike mai zurfi kafin amincewa da sakin kuɗaɗen domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon kuɗaɗen.
Kwamishinan ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa fifita jin daɗin masu fansho duk da ƙalubalen da jihar ke fuskanta.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da kuɗaɗen sun nuna farin cikinsu tare da bayyana matakin a matsayin babban sauki ga rayuwarsu da iyalansu.
Comments
Post a Comment