Gwamnatin Tarayya Ta Rage Kuɗin Jirgin Kasa Da Kashi 50% Domin Bukukuwan Sallah

Gwamnatin Tarayya ta amince da rage Kuɗin jirgin ƙasa da kashi 50 cikin 100 domin sauƙaƙa wa al’ummar Najeriya zirga-zirga yayin bukukuwan Eid-el-Kabir.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Osima Gift Seddon ya fitar a madadin Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗar da Jama’a na Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya.

Sanarwar ta bayyana cewa rage Kuɗin zai fara aiki daga ranar Talata, 26 ga watan Mayu, zuwa ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2026.

Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri, Injiniya Funsho Adebiyi, ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na rage wa ‘yan Najeriya raɗaɗin Kuɗin sufuri a lokacin Sallah, lokacin da yawan matafiya ke ƙaruwa.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO