Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Shirin TVET na 2026, Za a Ba Matasa Horon Sana’a da Tallafin ₦22,500 Duk Wata

Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara shirin horas da sana’o’i na Technical and Vocational Education and Training (TVET) na shekarar 2026 domin bai wa matasan Najeriya damar koyon sana’o’in dogaro da kai kyauta.

A ƙarƙashin shirin, mahalarta za su samu horo kyauta a cibiyoyi da aka amince da su a faɗin ƙasa, tare da tallafin kuɗi na ₦22,500 duk wata yayin horon.

Haka kuma, bayan kammala horaswar, wasu daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin za su samu kayan fara sana’a da takardun shaidar ƙwarewa da gwamnati ta amince da su.

An bayyana cewa horaswar za ta ɗauki tsakanin watanni shida zuwa shekara guda, gwargwadon irin sana’ar da aka zaɓa.

Shirin ya fi karkata ga matasa marasa aikin yi, masu son koyon sana’a, masu neman dogaro da kai da kuma waɗanda ke son fara ƙananan sana’o’i cikin gaggawa.

Domin cancanta, dole ne mai nema ya kasance ɗan Najeriya, ya mallaki NIN da BVN, sannan ya nuna ƙwazo da shirye-shiryen kammala horon.

Gwamnati ta buƙaci masu sha’awar shiga shirin da su garzaya wajen cike fom ɗin neman shiga, saboda yawan guraben horaswar na da iyaka.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO