GAGARUMIN LABARI: NAERLS Ta Ƙaddamar da Babban Shirin Ceto Noma da Lafiyar Ƙasa a Afirka Ta Yamma

Ma'aikatar Bincike da wayar da kan manoma da kuma yaɗa dabarun noma ta ƙasa, NAERLS, da ta ke a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya, ta gudanar da taron haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki kan shirin C4SEAS na ƙarfafa tsarin bada shawarar noma da kula da lafiyar ƙasa a Afirka ta Yamma.

A yayin taron da aka gudanar a Samaru, Zaria, shugabannin jami’ar da masana noma sun jaddada muhimmancin bunƙasa ilimi da horaswa ga manoma domin magance matsalolin noma da sauyin yanayi.

Masu jawabi sun bayyana cewa shirin na C4SEAS zai taimaka wajen inganta ƙwarewar jami’an bada shawarar noma, da samar da kayan horaswa da kuma tallafa wa manoma da sabbin hanyoyin kula da ƙasa domin ƙara yawan amfanin gona a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO