FIFA Ta Tabbatar: Jay-Jay Okocha Har Yanzu Ne Ke Rike da Tarihin Yanka Mafi Yawa a Wasan Kofin Duniya
Hukumar kula da kwallon ƙafa ta duniya (FIFA) ta sake tabbatar da cewa fitaccen tsohon ɗan wasan Najeriya, , har yanzu shi ne ke riƙe da tarihin yin yanka (dribble) mafi yawa cikin wasa guda a gasar Kofin Duniya ta FIFA.
A cewar FIFA, Okocha ya yi nasarar wuce 'yan wasa sau 15 ta hanyar yanka (dribble) a wasan zagaye na biyu tsakanin Najeriya a gasar Kofin Duniya ta shekarar 1994 da aka gudanar.
Wannan gagarumin tarihi ya kasance ba a karya shi ba fiye da shekaru 30, lamarin da ke nuna irin bajintar da Okocha ya nuna a lokacin da yake taka leda.
Okocha, wanda ake kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasan Afirka da suka taɓa taka kwallo, ya shahara wajen iya sarrafa ƙwallo, saurin motsi da kuma ƙwarewar wuce abokan hamayya cikin sauki.
Duk da fitowar manyan taurarin ƙwallon ƙafa daga sassa daban-daban na duniya a cikin shekaru da dama da suka gabata, babu wani ɗan wasa da ya samu damar karya wannan tarihi a wasa guda a gasar Kofin Duniya.
Sake tabbatar da wannan tarihi da FIFA ta yi ya ƙara nuna muhimmiyar gudunmawar da Jay-Jay Okocha ya bayar ga ƙwallon ƙafar Najeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.
Comments
Post a Comment