Da Ɗumi-Ɗumi: APC Ta Tsayar da Hon. Yakubu-Danladi a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kwara
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta zaɓi Rt. Hon. Salihu Yakubu-Ɗanladi a matsayin ɗan takararta na gwamnan Jihar Kwara a zaɓen 2027.
Ɗanladi mai shekaru 40, wanda aka haifa ranar 31 ga watan Mayun 1985, zai cika shekaru 41 a mako mai zuwa. Shi ƙwararren Injiniya ne kuma gogaggen ɗan siyasa da ya kafa tarihi a shekarar 2019 bayan an zaɓe shi a matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara yana da shekaru 34 kacal.
An sake zaɓensa a matsayin Kakakin Majalisar a shekarar 2023, lamarin da ya ƙara tabbatar da irin karɓuwar da yake da ita a siyasar jihar.
Rt. Hon. Salihu Yakubu-Ɗanladi yana wakiltar mazaɓar Ilesha-Gwanara/Baruten a Majalisar Dokokin Jihar Kwara ƙarƙashin jam’iyyar APC, inda ya shahara wajen jagoranci da haɗa kan ‘yan majalisar.
Rahotanni sun bayyana cewa fitowarsa a matsayin ɗan takarar APC ta samu cikakken goyon bayan gwamnan jihar mai barin gado, AbdulRahman AbdulRazaq, wanda ake ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasararsa.
Salihu ya kammala karatunsa a Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna a Jihar Neja, inda ya samu digiri a fannin Injiniyan Lantarki. Kafin shigarsa siyasa, ya yi aiki a matsayin Injiniya tare da nuna ƙwarewa a harkokin shugabanci da gudanarwa.
Comments
Post a Comment