Da Ɗumi-Ɗumi: Amaechi Ya Ƙalubalanci Tinubu Kan Wanda Ya Kai Buhari Mulki

Tsohon Gwamnan Jihar Rivers kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya musanta iƙirarin Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, cewa shi ne ya sanya marigayi Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2015.

Amaechi, wanda yanzu yake daga cikin fitattun ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya bayyana cewa shi ne ya jagoranci manyan fafutukar yaƙin neman zaɓen Buhari a lokacin da aka kayar da gwamnatin PDP bayan shekaru 16 tana mulki.

Tsohon ministan ya ce a matsayinsa na Darakta Janar na yaƙin neman zaben Buhari a shekarar 2015, ya taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan ‘yan adawa, tsara dabarun yaƙin neman zaɓe da kuma gudanar da manyan ayyukan siyasa da suka kai ga nasarar Buhari.

Amaechi ya bayyana cewa bai taɓa son yin magana kan batun ba tun farko saboda yana cikin gwamnatin Buhari a lokacin, kuma baya son tayar da rikici a cikin jam’iyyar APC da gwamnati.

Sai dai yanzu ya fito fili yana ƙalubalantar iƙirarin Tinubu, wanda tun kafin zaɓen 2023 yake cewa shi ne ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Buhari ya zama shugaban ƙasa.

Amaechi dai ya taɓa neman tikitin takarar shugaban ƙasa a APC a shekarar 2022 amma ya sha kaye a hannun Tinubu, kafin daga bisani ya fara sukar gwamnatin yanzu tare da komawa ɓangaren adawa.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO