"Da ace na bar babban birnin ƙasa a Lagos da Arewa ba ta Samu Cigaban da ta Samu Ba"— IBB

Tsohon Shugaban Mulkin Soja na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce da ya bar babban birnin ƙasa a Lagos bai dawo da shi kusa da Arewa ba, da Arewa ba ta samu irin matsayin da ta samu ba yanzu. 

Ibrahim Babangida ya faɗi hakan ne a yayin da ya ke kira ga shugabannin Arewa da su haɗa kai domin ceto yankin daga halin da yake ciki na koma baya da rugujewa. 

A wani jawabi da ya gabatar a safiyar yau, Babangida ya bayyana damuwarsa kan yadda manyan dattawan Arewa ke ci gaba da rasuwa, yana mai cewa hakan na nuna muhimmancin sabbin shugabanni su tashi tsaye domin kare martaba da makomar yankin.

“Kun ga yadda manyan dattawan yankinmu suke ta rasuwa, malamai, ‘yan siyasa da sauran fitattun mutane. Ni kaina yanzu ina jin jikina ya yi rauni, ban ma san ko zan kai ƙarshen wannan shekarar ba. Fatanmu shi ne Allah Ya karɓi ƙarshenmu cikin imani,” in ji shi.

IBB ya kuma tuna da irin rawar da gwamnatinsa ta taka wajen bunƙasa Arewa, inda ya bayyana cewa matsar da babban birnin tarayyar Najeriya daga Lagos zuwa Abuja na daga cikin manyan matakan da suka taimaka wajen ƙarfafa matsayin yankin Arewa a ƙasar nan.

“Da ace na bar babban birnin ƙasa a Lagos ban dawo da shi kusa da Arewa ba, watakila yau ba za a ma san Arewa da irin matsayin da take da shi ba. Alhamdulillah mun yi namu iya ƙoƙari, yanzu lokacinmu yana ƙarewa. Ina kira ga shugabannin Arewa su haɗa kai su ƙwato yankinmu, domin ba mu da wani yankin da ya wuce shi,” ya ƙara da cewa.

Kalaman na Babangida na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan matsalolin tsaro, talauci, rashin aikin yi da kuma ƙarancin haɗin kai da suka addabi yankin Arewa a Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO