Bayan Shekaru 12 Tana Neman Haihuwa, Mata Ta Haifi ’Yan Biyar A Ethiopia

Wata mata mai shekaru 35 a ƙasar Ethiopia mai suna Bedriya Adem ta haifi jarirai biyar lokaci guda bayan shafe shekaru 12 tana neman haihuwa ba tare da nasara ba.

Rahotanni sun bayyana cewa matar ta haifi jariran ne a Asibitin Hiwot Fana Specialized Hospital da ke yankin Harari na ƙasar Ethiopia.

An ce jariran sun haɗa da maza huɗu da mace ɗaya, kuma an haife su ne ta hanyar tiyata (Caesarean Section).

Likitoci sun tabbatar da cewa mahaifiyar tare da jariran na cikin ƙoshin lafiya, duk da cewa an ajiye jariran a ƙarƙashin kulawar musamman saboda ƙananan jikinsu.

Abin da ya ƙara ɗaukar hankali shi ne yadda aka ce cikin ya samu ne ta hanyar halitta ba tare da amfani da fasahar IVF ko magungunan ƙara haihuwa ba, lamarin da masana suka bayyana a matsayin abu mai matuƙar wuya a duniya.

Matar ta bayyana farin cikinta bayan shekaru masu yawa na jiran samun haihuwa, tana mai cewa:
“Na roƙi Allah ya ba ni yaro ɗaya kawai, amma Ya ba ni biyar.”

Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa likitoci tun farko sun yi zaton jarirai huɗu ne kawai ke cikin, sai dai aka gano na biyar yayin aikin haihuwar.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO