🟥Atiku Ya Musanta Jita-Jitar Ficewa Daga ADC Zuwa NDC
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi Æ™arin haske kan raÉ—e-raÉ—in da ke cewa zai fice daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin komawa Nigeria Democratic Congress (NDC), inda ya bayyana cewa babu wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da hakan.
Rahotanni sun nuna cewa jita-jitar ta karu ne bayan Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun fice daga ADC tare da shiga NDC a hukumance a Abuja, lamarin da ya janyo sabbin hasashe kan makomar manyan ‘yan adawa gabanin zaben 2027.
Majiyoyi na kusa da Atiku sun tabbatar da cewa har yanzu yana cikin ADC, kuma bai ɗauki wani mataki na sauya sheka ba. Sai dai sun ce ana ci gaba da tuntuɓa da shawarwari tsakanin jagororin adawa kan yiwuwar kafa ƙawance mai ƙarfi.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa wannan ci gaba na iya yin tasiri ga tsarin siyasar adawa, musamman yadda ake ƙoƙarin haɗe ƙarfi domin tunkarar zaɓe mai zuwa.
Comments
Post a Comment