Ƙarshen Duhu Ya Zo? Dangote Ya Shirya Gwangwaje Najeriya Da Wutar Lantarki MW 20,000
Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na iya taimakawa wajen rage matsalar ƙarancin wutar lantarki da ta daɗe tana addabar ƙasar, tare da buɗe sabon babi na ci gaba a ɓangaren makamashi.
Masu sharhi kan harkokin tattalin arziƙi sun alaƙanta wannan ci gaba da sauye-sauyen manufofi da gwamnatin shugaban ƙasa ta aiwatar, waɗanda suka bai wa masu zuba jari masu zaman kansu damar shiga harkar samar da wutar lantarki domin bunƙasa ɓangaren.
Ana sa ran cewa idan aka aiwatar da wannan shiri yadda ya kamata, Najeriya za ta iya samun ingantacciyar wutar lantarki mai ɗorewa cikin shekaru masu zuwa, lamarin da zai taimaka wajen haɓaka tattalin arziƙi da rage matsalolin da ke tattare da rashin wuta a faɗin ƙasar.
Comments
Post a Comment