‘Yan Ƙwacen Babur Sun Sare Hannun Wani Malami a Kano
Wasu da ake zargi ‘yan fashin babur ne sun sare hannun wani malami mai suna Isah Sallama yayin wani mummunan hari a ƙaramar hukumar Bunkure da ke jihar Kano.
Rahotanni sun ce maharan sun kai masa hari ne domin ƙwace masa kaya, inda suka yi masa munanan raunuka kafin su tsere. An garzaya da shi asibiti domin samun kulawar gaggawa, yayin da jami’an tsaro suka fara bincike don kamo waɗanda suka aikata laifin.
Comments
Post a Comment