‘Yan Sanda Sun Kashe Ɗan Ta’addan Lakurawa, Sun Ceto Shanu 33 a Kebbi
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa jami’anta sun kashe wani da ake zargin ɗan kungiyar ta’addanci ta Lakurawa, tare da daƙile yunƙurin sace shanu guda 33 a kan hanyar Kamba zuwa Kangiwa a ƙaramar hukumar Dandi ta jihar.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa jami’an ta sun samu sahihan bayanan sirri kan cewa wasu ‘yan ta’adda na shirin kwashe shanun da suka sace domin tsallaka su zuwa wani wuri. Nan take aka tura jami’an tsaro domin tare su a kan hanyar.
Rahotanni sun ce da ‘yan ta’addan suka hango jami’an tsaro, sai suka buɗe musu wuta, lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu. A yayin artabun, jami’an ‘yan sanda sun kashe ɗaya daga cikin maharan, yayin da sauran suka tsere cikin daji ɗauke da raunukan harbin bindiga.
Rundunar ta ce an samu nasarar ƙwato shanu guda 33 da maharan suka yi yunƙurin sacewa, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin gano masu su domin mayar musu da dukiyarsu.
Haka kuma, ta tabbatar da cewa jami’an tsaro sun ƙaddamar da farautar sauran ‘yan ta’addan da suka tsere, domin cafke su tare da kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da satar shanu a yankin.
Rundunar ‘yan sandan ta ƙara jaddada ƙudurinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da yin kira ga mazauna yankin da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan duk wani motsi na masu aikata laifi.
Comments
Post a Comment