‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Sashen Magunguna na Asibiti a Jihar Zamfara
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace Shugaban Sashen Magunguna na Babban Asibitin Nasarawa da ke ji har Zamfara a wani sabon hari da ya ƙara jefa fargaba a zukatan ma’aikatan lafiya da mazauna yankin. 🚨
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a Nasarawa da ke ƙaramar hukumar Maru, inda wasu ɗauke da makamai suka mamaye yankin tare da yin awon gaba da babban jami’in asibitin zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Shaidu sun ce maharan sun kai harin cikin gaggawa, lamarin da ya haddasa firgici a tsakanin al’umma, inda wasu mazauna yankin suka ruga domin tsira da rayukansu. Har yanzu dai ba a fitar da cikakken bayani kan sunan wanda aka sace ba, amma majiyoyi sun tabbatar cewa shi ne ke jagorantar sashen Magunguna na asibitin.
Comments
Post a Comment