'Yan Bindiga Sun Kashe Liman Da Wani Mai Ibada, Sun Sace Mata a Zamfara, Sojoji Sun Kama Mai Safarar Alburusai


Zamfara – Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani liman tare da wani mai ibada a wani hari da suka kai kan wani masallaci, sannan suka sace mata da dama a ƙauyen Sabuwar Tunga da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da maharan suka shiga ƙauyen dauke da makamai, inda suka bude wuta kan masu ibada bayan kammala sallar dare.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun harbe limamin masallacin tare da wani mutum guda a cikin masallacin, lamarin da ya jawo tashin hankali a yankin. Bayan haka, maharan sun shiga gidaje suna kwashe mata, ciki har da matan aure da ‘yan mata.

An kuma ruwaito cewa maharan sun kai hare-hare a wasu ƙauyuka makwabta, ciki har da Gommanan da ke yankin Gabake, inda suka sake yin garkuwa da wasu mata.

A wani samame na daban, sojojin rundunar 1 Brigade tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na sa-kai sun samu nasarar kama wani mutum da ake zargi da safarar alburusai ga ‘yan bindiga.

Rahotanni sun nuna cewa an kama wanda ake zargin ne a yankin Gusau, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Shinkafi domin kai kayan ga ‘yan bindiga.

Lokacin da aka binciki kayansa, jami’an tsaro sun gano cewa ya ɓoye alburusai a cikin galan ɗin manja.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO