Wani Mutum Ya Tone Kabarin ‘Yar’uwarsa, Ya Kai Ƙasusuwanta Banki Domin Karɓar Kuɗi

Wani mutum mai suna Jeetu Munda a ƙasar Indiya ya tayar da hankalin jama'a bayan da ya tone kabarin marigayiyar ‘yar’uwarsa tare da kai ƙasusuwanta banki, bayan jami’an bankin sun nace cewa sai mai asusun ta bayyana da kanta kafin a cire kuɗi.

Rahotanni sun ce mutumin ya yi ƙoƙarin cire kuɗi daga asusun ‘yar’uwarsa wadda ta rasu, amma rashin sanin hanyoyin doka ya sa ya ɗauki wannan mataki.

Jami’an ‘yan sanda sun isa wurin bayan faruwar lamarin, inda suka bayyana cewa mutumin bai san dokokin banki ba, tare da yin alƙawarin taimaka masa ya bi hanyoyin da suka dace domin karɓar kuɗin.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO