Ƙungiyar Amnesty International Ta Soki Wike Kan Barazanar Harbin Ɗan Jarida
Kungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bayan ya yi furucin barazanar harbin wani ɗan jarida yayin wata hira kai tsaye a tashar Arise TV.
Ƙungiyar ta bayyana kalaman a matsayin masu haɗari ga ‘yancin aikin jarida da dimokuraɗiyya, tare da buƙatar ministan ya janye furucin da kuma neman afuwar jama’a.
Lamarin ya jawo cece-kuce a faɗin Najeriya, yayin da masu rajin kare haƙƙin bil’adama ke gargaɗin cewa irin wannan furuci daga jami’in gwamnati na iya tayar da tsoro a tsakanin ‘yan jarida.
Comments
Post a Comment