🔥 TAKUN SAKA: “Katange Jiragen Ruwan Trump Ba Zai Durkusar da Iran Ba” — Lim Tean
Wani ɗan siyasa kuma mai sharhi kan harkokin siyasar duniya, Lim Tean, ya yi kakkausar suka kan matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka na ƙaƙaba katangar jiragen ruwa kan ƙasar Iran, yana mai cewa matakin “abin dariya ne” kuma ba zai yi tasiri ga tattalin arzikin Iran ba.
A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Lim Tean ya bayyana cewa Iran ta riga ta tanadi kusan gangar mai miliyan 158 a cikin tankokin ruwa sama da 96 da ke yawo a tekuna, lamarin da zai ba ta damar ci gaba da sayar da mai duk da katangar jiragen ruwa.
Ya kuma ƙara da cewa ƙasar China, wacce ke sayen kusan kashi 90% na ɗanyen man Iran, za ta iya ci gaba da karɓar mai har zuwa watan Yuli na wannan shekara, ko da katangar ta ci gaba.
Lim Tean ya yi gargadin cewa idan har aka ci gaba da rufe mashigar Hormuz zuwa watan Yuli, ƙawayen Amurka da ke dogaro da man fetur daga yankin Fashiya ne za su fi fuskantar matsala, ba Iran ba.
Har ila yau, ya yi hasashen cewa farashin man fetur a Amurka na iya kaiwa tsakanin dala $8 zuwa $9 kan galan ɗaya, abin da zai iya haddasa rikici a cikin gida har ma Majalisar Dokoki ta yi amfani da dokar gyara ta 25 (25th Amendment) domin cire Trump daga mulki.
A ƙarshe, Lim Tean ya nuna cewa ba zai yiwu Amurka ta ci gaba da wannan katanga har zuwa watan Yuli ba, yana mai cewa Amurkawa na neman cimma yarjejeniyar zaman lafiya cikin gaggawa, kuma wannan mataki wata dabara ce ta siyasa a yaƙin da yake ganin Trump na shan kaye a cikinsa.
Comments
Post a Comment