Soja Boi Ya Fitar da Saƙonnin Shigar Kuɗi, Ya Kalubalanci Rundunar Sojin Najeriya


Wani tsohon soja da aka fi sani da Soja Boi ya jawo cece-kuce bayan ya wallafa wasu saƙonnin shigar kuɗi da ya ce hujja ce ta albashin da yake karɓa a lokacin da yake aiki.

Soja Boi ya kuma ƙalubalanci rundunar Sojin Najeriya da ta fito fili ta bayyana cikakken tsarin albashin sojoji domin jama'a su san gaskiya.

Ya ce albashin sojoji, musamman ƙananan jami’ai, bai kai yadda mutane ke zato ba, yana mai cewa a shirye yake ya gabatar da ƙarin hujjoji idan rundunar ta musanta ikirarin nasa.

Har zuwa yanzu, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da cikakken martani kai tsaye kan wannan batu ba, yayin da lamarin ke ci gaba da jawo muhawara a tsakanin jama'a.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO