Shugabannin APC a Zamfara Sun Amince da Tazarcen Tinubu da Gwamna Lawal a Zaɓen 2027
Shugabannin jam’iyyar (APC) a Jihar Zamfara sun bayyana cikakken goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma Gwamnan jihar Dauda Lawal a babban zaɓen shekarar 2027.
An cimma wannan matsaya ne a wani babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar Asabar, 25 ga watan Afrilu, 2026, a Fadar Gwamnati da ke Gusau.
Taron ya haɗa manyan jagororin jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar, ciki har da tsoffin gwamnoni, zaɓaɓɓun jami’ai, dattawa, matasa da mata, da kuma wakilai daga ƙananan hukumomi 14 na jihar.
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Lawal ya bayyana cewa lokacin da ake ciki ya dace da shirye-shiryen siyasa, duba da cewa ana tunkarar babban zaɓen 2027. Ya ce sauya sheƙarsu zuwa jam’iyyar APC mataki ne na dabara domin ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya da kuma bunƙasa ayyukan ci gaba a jihar.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa tana mai da hankali wajen dawo da zaman lafiya, gina cibiyoyi masu ƙarfi da kuma samar da ayyukan ci gaba ga al’ummar Zamfara. Haka kuma ya jaddada cewa shugabanci ba wai muƙami kaɗai ba ne, illa hidima da bayar da gudummawa ga cigaban al’umma.
Gwamnan ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar da su kasance masu biyayya da ladabi, tare da kauce wa duk wani abu da zai haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar.
A ɓangare guda, tsoffin gwamnoni na jihar — Ahmed Sani Yarima, da Mahmud Aliyu Shinkafi, da Abdul'aziz Yari da kuma Bello Mohammed Matawalle — sun bayyana cikakken goyon bayansu ga jam’iyyar APC tare da amincewa da sake tsayawar Shugaba Tinubu da Gwamna Lawal a zaɓen 2027.
A cikin sanarwar bayan taron, an bayyana cewa mahalarta taron sun tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da ƙarfafa haɗin kan jam’iyya, inganta tsaro, da kuma shirye-shiryen tunkarar zaɓen shekarar 2027.
Comments
Post a Comment