Shugabannin APC Sun Kai Ziyara Gidan Tsohon Gwamnan Kano Shekarau

Wasu manyan jagororin jam’iyyar (APC) na ƙasa sun kai ziyara gidan tsohon gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a birnin Kano domin tattaunawa da shi kan yiwuwar komawarsa cikin jam’iyyar.

Rahotanni sun bayyana cewa tawagar jagororin jam’iyyar ta ƙasa ta je gidan tsohon gwamnan ne a wani yunƙuri na zawarcinsa da kuma ƙarfafa masa gwiwa ya shiga sahun jam’iyyar APC gabanin zaɓuɓɓukan siyasa masu zuwa.

Tawagar shugabannin jam’iyyar ta ƙunshi shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, tare da wasu manyan jami’an jam’iyyar da ba a bayyana sunayensu ba a hukumance.

Majiyoyi sun ce ganawar ta gudana ne cikin sirri, inda aka tattauna batutuwan siyasa da kuma makomar Malam Shekarau a fagen siyasar ƙasa, musamman dangane da sauye-sauyen siyasa da ake ci gaba da gani a Jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO