"Shugaba Trump Ya San Da ni" –InJi Ba'ameriken da Aka Cafke A Jos

Jos, Plateau – Alex Barbir, ɗan Ƙasar Amurka da aka kama a Jos bayan tashin-tashinar da ta yi sanadiyar asarar rayuka masu yawa a birnin na Jos, ya fitar da sanarwa mai ƙarfi ga jama’a, inda ya ce:

"Mutane na yaɗa labarai a kaina suna yi mun barazana, idan har wani abu ya same ni, za a sami babbar matsala. Ban ji tsoro ba! Shugaba Donald Trump ya san da zama na a nan, kuma mutanen Amurka sun san ina nan."

Barbir, wanda ake zargin yana da hannu a tashin hankali da rikice-rikice da suka afku a Jos, ya bayyana wannan jawabi ne yayin da mutane suka tsananta zargi a kansa cewa shi ne ke jagorantar rashin zaman lafiya a garin.

Jami’an tsaro sun tabbatar da kama Barbir a wani wuri da ba a bayyana ba a Jos, yayin da ake gudanar da bincike kan abubuwan da suka faru a lokacin rikicin. Sai dai Barbir ya tabbatar da cewa ba shi da tsoro duk da irin barazanar da ake yi masa, kuma yana kira ga duniya da ta lura da halin da yake ciki.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da Jihar Filato ke fuskantar ƙaruwar tashin hankali, inda al’ummomi da dama ke nuna damuwa kan tsaro da rayuwa a jihar. Har yanzu hukumomi na ci gaba da gudanar da bincike kan dalilan tashin hankalin da ya afku.

Masu sharhi a fagen tsaro sun ce, yadda Barbir ya fito fili yana nuna gadara, ana iya samun ɗimbin rudani idan ba a ɗauki matakin da ya dace ba.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO